Online counter

Babu inda ya kai Najeriya fatara da talauci a duniya – Jonathan

Babu inda ya kai Najeriya fatara da talauci a duniya – Jonathan

LABARAI DAGA 24BLOG
Jonatahan na wadannan kalamai ne cikin sakonsa day a fitar a shafinsa na tuwita na taya Najeriya da ‘yan kasar murnar zagayowar ranar samun ‘yan ci a karo na 58.
A sakon nasa, bayan ya yi murnar zagayowar wannan rana, ya kuma bayyana juyayinsa bisa yadda yanzu Najeriya ta zama shelkwatar fatara da talauci a fadin duniya baki daya.
Sai dai tsohon shugaba Jonathan ya karfafawa ‘yan Najeriya gwuiwar cewar halin fatara da talauci da kasar ke fuskanta ba zai dore ba saboda irin yadda mutanen Najeriya keda jajircewa wajen neman na kansu.
Na san cewar lamura sun yi matukar tsauri yanzu a Najeriya, musamman ganin yadda aka bayyana kasar a matsayin shelkwatar talauci ta duniya. Amma duk da haka na san cewar wuyar da ake ciki ba zata dore ba har abada.
A karshe ‘yan Najeriya ne zasu yi farinciki saboda irin juriya da karfin halin da suke da shi, musamman hakurinsu a yanayi na tsanan,” a cewar Jonathan.
Sannan ya cigaba da cewa, “zan takaita sakona na taya Najeriya murnar cika shekaru 58 da ‘yanci da wannan kalami: Bayan wuya sai dadi. Allah ya albarkaci Najeriya da dukkan jama’arta.
Ya zuwa yanzu fadar shugaban kasa bat a mayar da martini ga wannan kalamai na tsohon shugaba Jonathan ba.

Post a comment

0 Comments