APC ta ce INEC ba ta iya dakatar da 'yan takararta a Zamfara

LABARAI DAGA 24BLOG
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta jaddada cewa ta aika da sunayen 'yan takararta ga hukumar zabe ta INEC.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da ke bayani kan matsalolin da ta samu a wasu jihohi, Jam'iyyarAPC ta ce tana da 'yancin mika sunayen 'yan takararta na Zamfara kuma hakkin hukumar zabe ne ta karba.
Ta ce INEC ba za ta iya hana wa 'yan takararta shiga zabe ba a Zamfara.
Kuma ta ce ikirarin da hukumar zaben kasar ta yi game da sha'anin 'yan takararta a Zamfara ba daidai ba ne kuma za ta ci gaba da bin matakan da suka dace domin tabbatar da ganin hukumar ta yi abin da ya dace.
A farkon watan Oktoba ne hukumar INEC ta ce jam'iyyar APC ba ta da hurumin tsayar da 'yan takarar gwamna da na 'yan majalisar jiha da na tarayya a zaben 2019, saboda ta kasa gudanar da zaben fitar da 'yan takara.
Sai dai kuma jam'iyyar APC ta dage kan cewa tana da 'yan takara kuma tuni ta mika sunayensu ga hukumar zaben.