APC 5 sun wanke kansu daga zargin kulla tuggu akan Buhari da Oshiomhole

LABARAI DAGA 24BLOG
A jiya Talata wasu gwamnoni 5 na jam'iyyar APC suka wanke kansu tatas daga zargin kulla tuggu na shigo-shigo ba zurfi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ana zargin gwamnonin da kulla tuggun kawo zagon kasa ga kudirin shugaba Buhari na sake neman kujerarsa da kuma kulla kitimurmurar tsige Oshiomhole daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar.
Kungiyar mai goyon bayan tazarcen Buhari yayin gudanar da zanga-zanga a babban ofishin jam'iyyar APC dake birnin tarayya domin nuna goyon bayanta ga shugaban jam'iyyar, ta zargi wasu gwamnoni 5 da kulla tuggu da ya sabawa ka'ida da al'ada ta kowace jam'iyya.
Gwamnonin APC 5 sun wanke kansu daga zargin kulla tuggu akan Buhari da Oshiomhole
Kungiyar ta bayar da sunayen gwamnonin da ta ke zargi da suka hadar da; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Kayode Fayemi na jihar Ekiti da kuma Jibrilla Bindow na jihar Adamawa.
Ekweremadu
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnonin sun tsarkake kansu daga wannan zargi inda suka bayar da tabbacin goyan bayan su dari bisa dari baya ga girmamawa ta kololu da suke da ita ga shugaba Buhari da kuma shugaban jam'iyyar.
kuma ruwaito cewa, jam'iyyar APC reshen jihar Enugu ta fatattaki daya daga cikin jiga-jigan ta kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Onyemauche Nnamani, bisa laifukan rashin da'a.