Online counter

Ana binciken Arda Turan bayan yayi dambe a cikin a gidan rawa

Ana binciken Arda Turan bayan yayi dambe a cikin a gidan rawa

LABARAI DAGA 24BLOG
Mun samu labari cewa ‘Dan wasan nan na tsakiya na ainihin Kungiyar Barcelona ta kasar Sifen ya shiga wani mawuyacin hali inda ake tunani za a iyadaure sa a gidan yari har na tsawon shekaru 12 idan aka same shi da rashin gaskiya.
Ana dai zargin ‘Dan wasan yayi dambe da wani mutumi ne a gidan rawa. Yanzu haka dai idan aka same shi da laifin fada da wani shararren Mawaki mai suna Berkay Sahin, za a iya yanke masa tsawon shekaru na zaman kaso a Turkiyya.
Rahotanni su na yawo cewa ‘Dan wasan yayi dambe ne da wani fitaccen Mawaki da ke Garin Istanbul cikin dare a wani gidan rawa. Yanzu dai Jami’an ‘Yan Sandan Kasar sun soma binciken abin da ya faru tun a makon can da ya gabata.
‘Dan wasan mai shekaru 31 yana taka-leda ne yanzu haka a Kungiyar Basaksehir da ke babban Birnin Istanbul. Kungiyar ta dauko aron ‘Dan wasan ne bayan ya gaza samun damar buga wasa gaba daya a Kungiyar Barcelona ta Kasar Sifen.
Jaridun Turai sun bayyana cewa Matar wannan Mawaki Sahin ce ta jawo fadan inda har ta kai Turan ya zaro bindiga yayi barazanar harbi. A nan-take dai aka zarce da Sahin asibiti bayan ‘Dan kwallon yayi masa mugun rauni a kan karon hancin sa.

Post a Comment

0 Comments