An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da sassauta dokar hana fita ta sa'a 24 da aka sanya a jihar ranar Lahadi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter, sai dai ba duka sassan jihar ba ne aka sassauta dokar.
Gwamnan ya fitar da sanarwar ce bayan da aka kammala taron majalisar tsaro ta jihar.
An sassauta dokar a birnin Kaduna, daga karfe daya na rana zuwa karfe biyar na yamma a yau Talata.
Wannan na nufin kenan mutane za su iya zirga-zirgarsu da harkokinsu a birnin tsakanin karfe dayan rana zuwa karfe biyar na yamma.
Amma sanarwar ta ce bayan karfe biyar na yamman yau Talata, za a koma kan tsarin hana fita na sa'a 24 har illa ma sha Allahu.
Har ila yau, gwamnan ya ce akwai unguwannin da dokar hana fita za ta ci gaba da aiki wadanda su ne Kabala West da Kabala Doki da Narayi da Maraban Rido.
Sanarwar ta kuma ce an rage tsawon sa'o'in hana fita a yankunan Kasuwan Magani da Kujama, wuraren da rikicin ya samo asali.
Hanyoyi hudu da za a bi a magance rikicin Kaduna
Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Kaduna ya shafa
Jagoran awaren Biafra Nnamdi Kanu ya bayyana a Isra'ila
A ranar Litinin da dare ne gwaman ya sanar da mutanen jihar cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan a yayin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai.
Amma akwai rahotannin da ke cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 26.
Hakazalika ya ce an kama mutane da adama da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin.
Ya kuma ce za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin tayar da wannan hatsaniyar.