An sace 'yan mata tagwaye da aka kusa bikinsu a Zamfara

LABARAI DAGA 24BLOG
An sace wasu 'yan mata tagwaye lokacin da suke kan hanyarsu ta kai wa 'yan uwa da abokan arziki ankon bikinsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Mataimakin Shugaban karamar hukumar Zurmi Abubakar Muhammad ya ce tagwayen wadanda ake shirye-shiryen aurensu suna cikin mutane bakwai da aka sace a garin Dauran da ke jihar Zamfara.
"A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi ne aka sace mutanen bakwai - wato maza hudu, mata uku.
"Nan kusa gare mu ma an sace namiji guda, mace guda wato nan Birnin Tsaba ke nan," in ji shi.
An hana Buhari da Atiku kashe fiye da ₦5 biliyan a zaben 2019
Yadda gwamnatin Najeriya ke raba wa 'talakawa' N5,000
Me gwamnatin Najeriya ta ce kan kayyade iyali?
Ya ci gaba da cewa: "A garin Moriki an ma an dauki mutum uku da wadansu da aka sace ciki har da wani kansila."
Har ila yau ya ce an yi magana da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci a "biya su naira miliyan 100 kafin su sako 'yan tagwayen."
Daga nan ya bukaci da a kawo musu dauki don kawo karshen matsalar.
Zamfara tana daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.
Karin bayani game da Zamfara:
Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
Take: Noma tushen arzikinmu
Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
Musulmi ne mafi yawa
Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000.