An aika wa Obama da Clinton 'sakon bam'

LABARAI DAGA 24BLOG
An aika wani abu da ake zargin bam ne ga tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar kasar Hillary Clinton, kamar yadda ta bayyana.
Wannan yana zuwa ne kwana biyu bayan an tsinci bam a gidan fitaccen dan kasuwa George Soros a wajen birnin New York.
Wasu masana masu kula da sakonnin da ake aike wa tsofaffin jami'an Amurka ne suka gano hakan.
Sai dai zuwa yanzu ba a san wurin da aka gano sakon ba tukuna.
Sakon farko dai an aika shi ga adireshin Misis Clinton a ranar 23 ga watan Oktoban, kamar yadda hukumomin tsaron sirrin kasar Amurkan suka bayyana.
"A safiyar yau, 24 ga watan Oktoba, aka aike da sako na biyu ga tsohon Shugaban kasar Barack Obama amma jami'an tsaron sirrin kasar sun bankado shi a birnin Washington DC," in ji wata sanarwa daga hukumar tsaron sirrin kasar.
"Duka sakonnin an bankado su ne kafin a aike wa wadanda aka nufa da su," in ji sanarwar.