Amurka ta haifar da faduwar hannayen jarin duniya

LABARAI DAGA 24BLOG
Kasuwannin hannun jari na Asia sun kara faduwa, bayan ruftowar da ta Amurka ta yi.
Kasuwar Nikkei ta Japan ta yi kasa da kusan kashi uku cikin dari a farkon budewarta haka ma ta Hong kong da Shanghai duka sun fadi.
An bayyana faduwar mafi muni tun 2011 inda ta shafe dukkanin ribar da da aka samu a kasuwar hannun jarin Amurka a bana.
kasuwar Amurka ta rufe da faduwa ne a ranar Laraba kusan kashi biyu da rabi cikin dari, bayan kasuwar ta cira sama a farkon watan nan.
Faduwar kasuwar Amurka ce ta haifar da faduwar darajar hannayen jarin a yankin Asiya.
Faduwar ta shafi kasuwar Japan da Hong kong da Shanghai da Koriya ta Kudu da Australia, haka ma faduwar ta shafi hannayen jarin China.
Masu nazari na ganin, karuwar kudin ruwa da raguwar harkokin gine-ginen gidaje da kuma yakin kasuwanci da Amurka ke yi da China su ne sanadin rashin tabbas na kasuwar.
Shugaba Trump dai ya dade yana ikirarin cewa habakar kasuwar hannun jarin manuniya ce ga nasarar manufofinsa.
Masana na ganin har da fargabar rikicin siyasa da aka shiga a Amurka ya kara haifar da faduwar darajar hannayen jarin.