Abun kunya: Yadda wasu 'yan mata 2 suka kacame da fada saboda saurayi a Najeriya

LABARAI DAGA 24BLOG
- Yadda wasu 'yan mata 2 suka kacame da fada a bakin titi
- Suna fada ne dai saboda saurayi
- Wasu na ganin wannan abun kunya ne
Wani faifan bidiyo da yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani na wasu 'yan mata tsala-tsala suka ta fada a tsakanin su saboda saurayi ya na ta yawo a kafafen sadarwar zamani tamkar wutar jeji.
Abun kunya: Yadda wasu 'yan mata 2 suka kacame da fada saboda saurayi a Najeriya (Bidiyo)
Kamar dai yadda wani namiji da ya dauki 'yan matan suna fadan kuma ya yada a dandalin sadarwar zamani, ya bayyana cewa abun takaicin da ya saka matan fada shine wani saurayin da da alama ya yaudare su su duka kuma ya tafi ya bar su.
Legit.ng Hausa dai ta samu cewa da alama saurayin kam ba ta su yake yi ba domin kuwa bai ma a wurin da 'yan matan ke sai da halin nasu suna fada a bainar jama'a.
A faifan bidiyon dai, 'yan matan suna ta fada ne da zage-zage inda kuma har ma sun kusa zama a tsirara sakamakon yayyaga kayan jikin su da suka yi.