Abinda ke haddasa ciwon basur - kwararriyar Likita

SANARWA DAGA 24BLOG
Wata kwararriyar likita, Dakta Nkechi Anthony, da ke zaune a Abuja ta bayyana cewar yawan ci da shan kayan kwalam da makulashe na zamani na daga cikin abubuwan da ke jawo kamuwa da cutar basur ko dan kanoma, kamar yadda wasu ke kiran shi.
Kazalika Dakta Nkechi ta bayyana cin cima mai tauri da babu ganye ko ruwa-ruwa cikinta da cewar na cushe ciki tare da saka bayan gida ya yi tauri, lamarin da shi ma na haifar da cutar basir.
Likitar ta kara da cewar, da yawan mutane ba su damu da cin abubuwan da su ke hana basur tasiri a jiki ba, kamar su ganye, da ya'yan itatuwa ba. Kazalika, ta bayyana shan isashshen ruwa mai tsafta na hana kamuwa da cutar basur.
Likitoci
Dakta Nkechi ta kara da cewa daga cikin alamun da mutum zai gane ya kamu da cutar basur shine ganin jini yayin bahaya ko kuma jin zafi yayin wanke dubura bayan yin bahaya. Sannan ta yi gargadi da guji yin amfani da takarda domin share dubura bayan yin bahaya, ta bayar da shawarar ake amfani da ruwa mai tsafta domin yin tsarkake dubura.
DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Hukumar ICPC ta cafke mahaifiyar Maryam Sanda a harabar kotu
Daga karshe ta shawarci jama'a da su daina kokarin rike bahaya yayin da su ka ji bukatar yin ta ya taso domin yin hakan na haifar da matsalolin da kan iya haddasa basur tare da gaggauta zuwa asibiti da zarar an ji canji a jiki.