Online counter

Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari-LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba yayi alkawarin cewa zai cigaba da yin adalci da daidaito wajen nade-naden mukamai daban-daban a gwamnatinsa.
Gidan talbijin din Channels ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wannan alkawarin ne a yayin wani tattaunawa da tawagar shugabanni da dattawan Akwa Ibom da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa 
“Na lura da godiyarku akan nade-naden mutanen jiharku da aka yi a gwamnatin tarayya.
“Na baku tabbacin cewa zan cigaba da yin adalci da daidaito a wajen nade-naden mukaman tarayya a dukkanin jihohin dake fadin kasar.”
SHIGA WANNANlDa duminsa: Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano
Shugaban kasar ya kuma sha alwashin yin Karin ayyukan ci gaba a jihar na Akwa Ibom da kudacin kasar baki daya.

Post a Comment

0 Comments