Online counter

Zaben raba gardama a Osun: Duba wasu sakamako da suka shigo hannU

Zaben raba gardama a Osun: Duba wasu sakamako da suka shigo hannU

LABARAI DAGA 24BLOG
A yau, Alhamis, 27 ga watan Satumba, ne mutanen jihar Osun suka komawa filin zabe domin kada kuri’unsu a zaben raba gardama na gwamnan jihar da aka yi zagayen farko ranar Asabar.
Yanzu haka Gboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC ne a gaba a zaben bayan lashe mafi rinjayen kuri’u a kananan hukumomin Ife ta kudu, Ife ta arewa da Osogbo.
Ana gudanar da zaben raba gardamar ne a mazabu 7 dake kananan hukumomin jihar Osun 4.
Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben
Orolu, mazaba ta 8, akwatu ta 4
APC 198
PDP 15
Orolu, mazaba ta 9, akwatu 3
PDP 64
APC 41
Karamar hukumar Ife ta kudu, akwatu ta 012
Adadin masu kada kuri’a da aka tantance 310
Kuri’ar da ta lalace 6
APC 283
APA 3
APGA 1
PDP 15
SDP 1
UPN 1
Mazaba ta 10, akwatu ta 02, karamar hukumar Ife ta arewa
APC 126
PDP 2
Mazaba ta 8, akwatu ta 10, karamar hukumar Ife ta kudu
APC 172
PDP 21
Mazaba ta 5, akwatu ta 17, karamar hukumar Osogbo
APC 299
PDP 165
Zamu cigaba da kawo karin sakamkon zaben da zarar sun shigo hannu

Post a comment

0 Comments