Online counter

Zaben gwamna: Nuhu Ribadu yayi karin haske game da batun janye takarar sa

Zaben gwamna: Nuhu Ribadu yayi karin haske game da batun janye takarar sa

LABARAI DAGA 24BLOG
Daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna na jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC kuma tsohon shugaban hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu ya karyata batun janyewar sa daga takarar.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kamfe din sa, Salihu Bawuro ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.
 A cikin takardar sanarwar, Salihu ya kara da cewa a da basu da niyyar yin wani bayani game da hakan sakamokon labarin wasu makiya ne kawai suka kirkira shi ro amma ganin cewa maganar na ta yawo a bakunan mutane ne ya sa suka ga ya dace su fayyace gaskiyar lamarin.
Daga karshe sai kuma ya bukaci dukkan magoya bayan su da su shirya tsaf domin ganin sun ga bayan gwamnatin rashin adalci da ake yi a jihar ta Adamawa.
A wani labarin kuma, Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa labaran da ake yadawa na cewa bai ji dadin kai zaben fitar da gwanin su ba a garin Fatakwal ba gaskiya bane.
Atiku wanda yace shi garin Fatakwal kusan gida ne a gare shi ya bayyana cewa baya ma bukatar masauki ko wani tsaro na musamman domin kuwa a yi wani bangare na rayuwar sa a garin a shekarun baya.

Post a comment

0 Comments