Online counter

Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar da Buhari ya samu

Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar da Buhari ya samu

LABARAI DAGA 24BLOG 
Fadar shugban kasa ta ce nasarar da shugaba Buhari a ya samu a zaben fidda gwani da a kayi ranar Juma'a a jihohin Najeriya inda aka zabi Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa tilo na jam'iyyar APC alamar nasara ne a zaben na 2019.
A sanarwar da ta fito daga bakin babban mai taimakawa shugaban kasa, Garba Shehu a ranar Asabar, ya ce miliyoyin 'yan jam'iyya da suka fito kwansu da kwarkwata domin jefawa shugaban kasa kuri'a na nuna cewa har yanzu Buhari yana da farin jini wajen mutane.
"Baya ga cewa wannan nasara ce ga shugaban kasa da jam'iyyar APC, nasarar kanta sako ce ga 'yan siyasa cewa kawo ayyukan cigaba da mulki mai inganci ya fi muhimmanci da siyasar raba kawunan al'umma'
"Darasin da da wasu sauran jam'iyyu za su iya koya itace ya kamata su fara koyi da tsarin shugabancin Muhammadu Buhari.
"Muna kuma mika godiyar mu ga dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin an samu wannan gagarumin nasarar," inji Garba Shehu.

Post a Comment

0 Comments