Online counter

Zaben 2019: An gano wanda Kwankwaso yake so ya kada Ganduje

Zaben 2019: An gano wanda Kwankwaso yake so ya kada Ganduje


-LABARAI DAGA 24BLOG
Ana sa ran cewa tsohon gwamNan Kano, Sanatan da ke wakiltar shiyyar Kano ta tsakiya kuma dan takarar tikitin takarar shugabancin kasar nan ta Najeriya a jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai bayyana surukin sa a matsayin wanda yake so ya zama Gwamnan Kano a 2019.
Tsohon Gwamnan dai kamar yadda muka samu, ana sa ran zai bayyana goyon bayan sa ne ga Abba Kabir Yusuf dake zaman surukin sa a matsayin wanda zai yi takara da Gwaman Kano kuma tsohon aminin nasa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben na 2019.
24blog ta samu cewa ana sa ran Gwamnan zai bayyanawa masoyan nasa haka ne a cikin karshen satin nan a gidan sa dake a garin Kaduna, jihar da ke makwaftaka da Kano inda kuma yakan gudanar da harkokin siyasar sa.
Sai dai kuma kamar yadda muka samu, ana tunanin wannan matakin nasa zai gamu da turjiya daga bangaren yan PDP din da basu goyon bayan tsohon gwamnan domin kuwa tuni wanda suke goyon bayan kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar a shekarar 2015, Sagir Takai ya nuna sha'awar sa.
A wani labarin kuma, Wani lauya dake ikirarin rajin kare hakkin bil'adama mai suna Mista Oleka Udenze dake zama a garin Abuja ya maka shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da wasu mukarraban gwamnatin sa game da shirin Atisayen rawar mesa na uku watau Operation Python Dance 3 a turance.
Shirin dai na 'Operation Python Dance' na zaman wani mataki da sojojin Najeriya suka dauka a watannin baya da nufin kakkabe dukkan wasu hatsabiban tsageru a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke son ballewa daga Najeriya.

Post a comment

0 Comments