Online counter

Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni

Za a zabi shugaba Buhari a 2019 ko don ayyukan da ya shimfida a kasar - Goni

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugabar kungiyar yakin zaben Buhari daga matakin farko GMBO, Dr. Fatima Mohammed Goni, ta ce kungiyar na da dalilai 150 da suka bada tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci ya zarce a babban zaben 2019 da ke tahowa.
A cewar ta, ayyukan da shugaban kasar ya samu nasarar kammala a cikin shekaru 3 wadanda suka shafi bangaren tattalin arziki, gina kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa sun isa Buhari ya koma ofishinsa a karo na biyu.
Goni, a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar da ke Abuja, ta ce idan aka cire 'yancin da doka ta baiwa shugaban kasar na sake tsayawa takara, ayyukan da ya shimfida a bayyane suke ga kowane dan Nigeria ya gani kuma ya tab
Ta kara da cewa kungiyar na kan shirye shirye na buga littafi dauke da dalilai 150 da suka tabbatar da cancantar Buhari na smaun damar yin tazarce a zaben 2019, duk da cewa ta bayyana damuwarta kan yadda rikici ke ballewa a wasu sassa na jam'iyyar APC, musamman a matakan jihohi.
Goni ta ce duk da tana farin ciki da irin salon shugabancin jam'iyyar karkashin Comrade Adams Oshiomhole, ya zamarwa shuwagabannin jam'iyyar dole su shawo kan matsalolin cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta musamman da ake fuskantar zabukan fitar da gwani.
"Jam'iyyar APC gida ne da ya hada kan kowa, bai kamata a samu rabuwar kawuna ba, sannan ya kamata a duba batun yawan 'yan takarar kujerar gwamamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar, idan da hali a kafa kwamiti da zai sulhunta tsakanin masu neman takarar kujerar," a cewar ta.
Haka zalika ta kara jaddada bukatar shuwagabannin jam'iyyar da su sanya baki akan rikicin da ke faruwa a jihar Imo tsakanin gwamnan jihar Rochas Okorocha da kuma tsohon mataimakinsa Osita Izunaso da ma Ifeanyi Ararumi, tsohon sakataren gudanarwa na jam'iyyar.

Post a comment

0 Comments