Online counter

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi ta

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi ta

LABARAI DAGA 24BLOG 
Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa Farfesa Hafiz ya sayi Fam din ne a sakatariya jam’iyyar PDP dake Abuja yau Laraba, 25 ga watan Satumba.
A karshen makon da ya gabata, Sanata Kwankwaso ya daga hannun tsohon kwamishanan ayyukan jihar Kano kuma Surukinsa, Abba Kabir Yusuf, a matsayin dan takaran gwamnan jam’iyyar daya tilo.
Yayi hakan ne saboda a tunaninsa Farfesa Hafiz Abubakar da Salihu Takai basu cancanci kujeran gwamnan jihar Kano ba a yanzu, sai dai na majalisa.
Wata majiya na kusa da Farfesa Abubakar ya bayyana cewa tsohon mataimakin gwamnan ya siya takardan takaran gwamnan ne domin fito-na-fito da Kwankwaso kan maganarsa cewa basu cancan
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar bazata birnin jihar Kano a jiya Litinin, 24 ga watan Satumba inda ya gabatar da jawabi ga mabiyansa gidansa da ke Milla Road.
Kwankwaso ya bayyana cewa dalilin zuwansa jihar Kano shine kwantar da kuran zaben sirikinsa matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.
Kwanakin nan, tsohon gwamnan ya zabi surukansa uku. Ya zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin zabinsa a shekarar 2019. Amma Kwankwaso yace su kwantar da hankalinsu.
Ya baayyana cewa ya zabi Abba Kabir Yusuf ne saboda shine yayi zanen dukkan gadojin da akayi jihar Kano musamman na Kofar Nasarawa.

Post a comment

0 Comments