Online counter

Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da zakaran zaben Osun, jam'iyyar APC ta yi nasara

Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da zakaran zaben Osun, jam'iyyar APC ta yi nasara

LABARAI DAGA 24BLOG
Tun misalin karfe takwas na afiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satumba 2018, jami'an hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun isa wurare bakwai da za'a karasa zaben jihar Osun.
Jami'an hukumar yan sanda da sauran jami'an tsaron sun mamaye wuraren domin tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ana gudanar da karashen zaben ne a wurare hudu:
1. Karamar hukumar Osogbo
2. Karamar hukumar Osogbo Ife ta arewa
3. Karamar hukumar Osogbo Ife ta kudu
4. Karamar hukumar Orolu
Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben
Orolu:
APC 280
PDP 122
Osogbo
APC 299
PDP 165
Ife ta kudu
APC 455
PDP 36
Ife
APC=126
PDP=2

Post a comment

0 Comments