KAYAN HADI
- Farar shinkafa
- Yis
- Sikari
- Gishiri
- Albasa
Yadda ake sarrafawa
1. Da farko za a wanke farar shinkafa a markada ta, ba lallai ne sai ta jiku ba sosai.
2. Sai a zuba yis da sikari da gishiri dai dai misali, sai a kada shi sosai.
3. A sanya shi a rana ya tashi, sai a yanka albasa kanana kanana a ciki
4. Za a iya zuba dafaffiyar shinkafa a ciki, amma sai an ga dama
5. A soya shi da mai a tanda
0 Comments