Abubuwan hadawa

 • Danyar kubewa gogaggiya
 • Albasa
 • Naman rago
 • Tattasai da attargu
 • Kanwa
 • Tafarnuwa
 • Citta

Yadda ake hadawa

 1. Da farko ki daura ruwa dan kadan a tukunya, sai ki kawo kubewarki da ki ka yayyanka kanana ko ki ka goge ta (gurza ta) ki zuba a ciki ki jefa ‘yar kanwa ki rufe ki bari yadahu har ya tsotse ki ajiye a gefe.

 1. Ki wanke albasa ki yanka, ki daura mai akan wuta ki sa albasa da tattasai attarugu da tafarnuwa isasshe da citta, ki sa nama ki sa maggi da ruwa ki rufe.

 1. Ki bari har sai naman ya dahu tubus, sai ki kawo wannan kubewa da ki ka dafa a gefe  ki hade su  ki rufe ki bari a wuta kadan (low heat) na kamar minti biyar sannan sai ki kwashe. 

  Wannan wata hanya ce ta sarrafa miyar kubewa irin na ‘yan borno..


  Za ki iya ci da sinasir ko biski ko tuwo (na shinkafa, dawa,alkama,madara,gero,semo ‘yar uwa har da tuwon cous-cous..

Abi lura

 • Dafa kubewa ta wannan sigar yana sa shi ya yi yauki sossai.
 • Sannan miyar yauki in ki naso tayi yauki kar ki cika kayan miya.
 • Tafarnuwa na gyara miyar kubewa.
 • Dafa kubewa daban tare da kanwa yakan sashi ya yi Kore shar a ido.. Ya kuma yi yauki sannan ya dahu cikin sauri.
 • 'Ya'yan kubewa suna sa kubewa yauqi.. Amma wasu basu sonshi kina iya ciresu.
 •