Abubuwan hadawa

 • Kwai
 • Attarugu
 • Albasa
 • Man girki
 • Maggi
 • Leda

Yanda ake hadawa

 1. Da farko zaki sami kwanki ki fasashi a kwanan ki mai kyau ki kadashi
 2. Sai ki zuba kayan hadinki: attarugu, da albasa wanda dama kin yi giretin nasu da sauran kayan dandano dai dai misali
 3. Sai ki dunga zuba kwan naki acikin leda kina yi  masa kamar kullin alalan leda
 4. Sannan sai ki dora ruwanki cikin tukunya ki dafa kullallen kwan naki
 5. Idan ya dahu sai ki kara fasa wani kwai, kuma ki cire wannan kwan naki na leda kina yankashi yankan tsakiya za kiga ya bada shef  din zuciya, watau ‘heart’ sai ki dunga tsomashi acikin wannan kwan naki
 6. Sai kuma ki soyashi a manki mai zafi sosai, amma ki yi suyar sama-sama don ya yi suya mai kyau