Online counter

Yan majalisa 9 sun sauya sheka a wata jihar APC

Yan majalisa 9 sun sauya sheka a wata jihar APC

-LABARAI DAGA 24BLOG 
'Yan majalisar jihar Oyo 9 ciki har da Mataimakin Kakakin majalisar jihar, Abdulwasi Musah sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyun APC, Accord Party da Labour Party zuwa jam'iyyar African Democratic Congress ADC a jihar.
Biyar daga cikin 'yan majalisar sun fice daga APC ne, uku kuma sun fice daga Accord Party sai guda daya ya fice da Labour Party kuma duk suka dunguma zuwa African Democratic Congress ADC.
Magatakardan Majalisar, Paul Bankole ne ya karanto wasikar sauya shekar na su zuwa ADC a zauren majalisar a zaman da akayi a jiya Talata.
Bayan mataimakin Kakakin majalisar, Sauran wanda suka sauya shekan sune Lukman Balogun, Bolaji Badmus, Azeez Billiaminu, Ganiyu Oseni, Olusegun Olaleye, Samson Oguntade da Muideen Olagunju.
Ficewar wadanda 'yan majalisar ya kawo adadin mambobin ADC a majalisar zuwa 12 yayin da jam'iyyar APC mai mulki tana da mambobi 18, ita kuma jam'iyyar PDP tana da mambobi 2 kacal.

Post a comment

0 Comments