Online counter

Yan bindiga sun hallaka wani tsoho dan shekara 62, sun jikkata 3 a Filato

Yan bindiga sun hallaka wani tsoho dan shekara 62, sun jikkata 3 a Filato


LABARAI DAGA 24BLOG
Majiyar 24blog ta ruwaito yan bindigan sun kashe wannan tsoho ne a yayin da suka kai farmaki a kauyen kwall dake yankin Miango cikin karamar hukumar Bassa na jahar Filato, haka zalika sun raunata mutane uku.
Kaakakin Yansandan jahar, Terna Tyopev ne ya tabbatar da haka a ranar Talata 18 watan Satumba garin Jos, inda yace yan bindigan sun kai harin ne a daren Litinin:
“Da misalin karfe 8 na safiyar Litinin ne wnai shugaban matasan Kwall, Robert Zarachi ya bamu rahoton hari da yan bindiga suka kai da misalin karfe 10:45 na daren Litinin zuwa gidan John Atu mai shekaru 62. A sakamakon wannan hari ne Atu ya gamu da ajalinsa, sa’annan wasu yayansa gud uku suka samu munana rauni a sanadiyyar harbe harben bindiga.” Inji shi.
Sai dai Kaakakin Yansandan yace tuni aka yi jana’izar John kamar yadda al’adun kabilar Irigwe ta tanadar, yayin da sauran yan uwannasa ke samun kulawa a Asibitin Enos dake garin Miango, daga karshe yace tun suka fara gudanar da bincike don kama maharan.
A wani labarin kuma, DSP Terna yace jami’an rundunar Yansandan jahar Filato sun samu nasarar kama mutane da suka kashe mutane uku a garin Gura Riyom dake karamar hukumar Jos ta kudu, inda ya bayyan sunayen wadanda aka kashe kamar haka; Aminu Angara, Aisha Musa da Daniel

Post a comment

0 Comments