Online counter

Yajin aiki: Mun yi asarar Miliyan 60 inji Kamfanin jiragen Air Peace

Yajin aiki: Mun yi asarar Miliyan 60 inji Kamfanin jiragen Air Peace

LABARAI DAGA 24BLOG 
Shugaban Kamfanin jiragen na Air Peace ya bayyanawa manema labarai cewa yajin aikin da manyan Kungiyoyin Ma’aikatan Najeriya wanda su ka hada da NLC na 'Yan kwadago da TUC na ‘Yan kasuwa su ka shiga ya masu mugun illa.
Allen Onyema wanda shi ne Shugaban Air Peace yace yajin aikin da aka shiga kwanan nan ya sa an rufe babban filin tashin jirgin sama na Najeriya na Murtala Muhammed da ke Legas inda aka hana jama’a tashi a Ranar Juma’ar nan.
Onyema yace Jagororin ‘Yan kungiyar kwadagon sun hana jama’a sakat tun safiya har zuwa karfe 11:00. Wanan dai ya sa fasinjojin jiragen saman da dama su ka hakura da tafiyar su. A dalilin haka dai dole jirage su ka fasa tashi a tashar.
Yajin aikin dai ya sa aka daga tashin jirage daga Legas bayan da ‘Yan kwadago su ka rikita ko ina su ka hana Ma’aikata aiki su na kade-kade da wake-waken su a filin tashi da saukar jirgin. Wannan ya sa dole kamfanin ya tafka asara.
Kamfanin jirgin dai ya rasa akalla Naira Miliyan 60 a sakamakon wannan abu da ya faru. Wani babban Jami’in kafanin mai suna Chris Iwarah ya nuna cewa ba su ji dadin hakan ba duk da cewa ba su hana a shiga yajin aiki a Kasar ba.
Ku na da labari cewa Kungiyar Malaman Jami’a ASUU ta caccaki Gwamnatin Tarayya inda har sun fara shirin shiga yajin aiki. ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi da ita a 2017.

Post a Comment

0 Comments