Online counter

Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado

Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado


LABARAI DAGA 24BLOG
Wutar rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina na ci gaba da ruruwa, a yayin da 'yan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar ke ci gaba da adawa da hukuncin shuwagabannin jam'iyyar na tsayar da Sanata Yakubu Lado a matsayin dan takarar gwamnanta ta hanyar nad'i ba tare da zaben fitar da gwani ba.
Wasu 'yan takara biyu, Abdullahi Garba Faskari da kuma Sada Ilu a cikin wata sanarwa daga Alhaji Dauda Kurfi, daraktan kungiyar kamfe ta Abdullahi Garba Faskari AGF, a madadin 'yan takarar, ya ce sakamakon amincewa da zaben nadin dan takara, mun amince da sharudda na cewa wani dan takara ba zai biya kudi don a zabe shi ba.
Sai dai ya ce sun gano cewar dukkanin sharuddan da suka gindayawa shuwagabannin jam'iyyar sun hau ta kansu sun zaune ba tare da amfani da ko daya ba, kuma da masaniyar shugaban jam'iyyar na jihar 
Sanarwar ta ce: "A don haka ne, muka yi watsi da wannan sakamako; haka zalika mun dawo daga rakiyar shuwagabannin jam'iyyar a matakin jihar, kuma ba zamu jure sa hannu a zaben fitar da gwani ba har sai idan uwar jam'iyyar ta kasa ta sanya hannu don ayiwa kowa adalci."
"Muna amfani da wannan kafar wajen bukatar shelkwatar jam'iyyar ta kasa da ta yi gaggawar sanya baki akan matsayar jam'iyyar a jihar Katsina, ma damar ana so a yiwa mambobin jam'iyyar dama daukacin al'umar jihar Katsina adalci," a cewar sanarwar.
cewa tuni dai dama wasu 'yan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar, Abdullahi Umar Tsauri, Musa Nashuni da kuma Arc. Ahmed Aminu Yar'adua suka yi 'tir!' da wannan zabe na tsayar da Lado a matsayin dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar.

Post a Comment

0 Comments