Online counter

Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

LABARAI DAGA 24BLOG 
Wasu 'yan bindiga a ranar Lahadi sun tare motoci biyar tare da sace dukkan mutanen dake ciki a kauyen Tashar Tsuntsaye dake a kusa da Kiriga, karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar dake rajin kare muradun 'yan garin na Birnin Gwari din watau Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance a turance, mai suna Ibrahim Nagwari.
mutanen da aka sace suna cikin wata motar haya ce kirar Golf da kuma wasu manyan motoci hudu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar hakan inda kuma ya bayyana cewa tuni jami'an su sun bazama neman barayin mutanen.
A wani labarin kuma, Daya daga cikin shugabannin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa a mataki na tarayya mai suna Mohammed Abdulrahman a cikin wata fira da yayi da wakilin jaridar Punch ya bayyana cewa shugaba Buhari yana nuna son kai da kabilanci a mulkin sa.
Mohammed din dai ya bayyana rashin gamsuwa da yadda shugaban kasar yake yin nade-naden sa musamman ma a bangaren tsaron kasar nan inda ya ce abin a duba ne ga dukkan mai hankali.

Post a Comment

0 Comments