Online counter

wani me neman takarar a jam,iyar APC a Kwara ya tona asirin cin hancin da Saraki ya yi masa alkawari idan ya bi shi PDP

wani me neman takarar a jam,iyar APC a Kwara ya tona asirin cin hancin da Saraki ya yi masa alkawari idan ya bi shi PDP

LABARAI DAGA 24BLOG
Sai dai Yahaya Seriki ya shaidawa manema labarai a babban birnin taraya Abuja cewar ya ki amince da dukkan tayin daaka yi masa.
Da ya ke tsokaci kan zargin da wasu ke yi masa na cewa shi dan leken asirin Saraki ne a APC, Yahaya-Seriki ya ce shi mutum ne mai kwazo da ya gina kansa kuma bashi da ubangida.
"Wasu na zargin cewa ina da alaka da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ko kuma ni dan leken asirinsa ne. Ina son tabbatar muku da cewa bani da wata alaka da shi kuma ba zan iya aiki tare da shi ba.
"A lokacin da mutane ke sauya sheka zuwa PDP a Kwara, labarai ya ishe Saraki cewar ba zan sauya sheka ba. Ya aiko Kwamishinan Harkokin Fada da Kiama ya kira zuwa gidansa.
"Na amsa kiransa inda muka hadu a gidansa da ke Lake Chad kuma a ranar ya min tayin mukammin mai bayar da babban mai bayar da shawara ta musamman amma na ki karba saboda akidar mu ba daya bane kuma ina kaunar jama'a ta," inji Seriki.
Yahaya Seriki ya kara da cewa baya goyon bayan yadda mutum daya zai rika juya jiha kamar gidan gadonsa hakan ya sa ya tsaya a APC ya cigaba da yiwa jam'iyya biyaya.

Post a comment

0 Comments