Online counter

Son kai da kabilanci: Wani dattijon Arewa yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Son kai da kabilanci: Wani dattijon Arewa yayi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

LABARAI DAGA 24BLOG 

Daya daga cikin shugabannin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa a mataki na tarayya mai suna Mohammed Abdulrahman a cikin wata fira da yayi da wakilin jaridar Punch ya bayyana cewa shugaba Buhari yana nuna son kai da kabilanci a mulkin s
Mohammed din dai ya bayyana rashin gamsuwa da yadda shugaban kasar yake yin nade-naden sa musamman ma a bangaren tsaron kasar nan inda ya ce abin a duba ne ga dukkan mai hankali..
Mohammed ya cigaba da cewa harkar tsaro na cigaba da fuskantar barazana a kasar nan duk kuwa da irin ikirarin da shugaba Buhari da mukarraban sa suke yi musamman ma idan akayi duba da irin makudan kudaden da suke kashewa.
Daga karshe kuma ya shawarci shugaban kasar da ya tabbatar da kawo karshen kashe-kashen da ake fama da shi musamman ma yankunan Arewacin kasar nan domin a cewar sa, shine ke da alhakin hakan.
A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya shiyyar jihar Osun dake a kudu maso yammacin kasar nan a ta bakin shugaban ta Mista Soji Adagunodo ta bayyana cewa yanzu haka ta yi nisa wajen tattara sunayen mambobin ta da suka mutu a zaben gwamnan jihar da ya gabata.
Mista Soji wanda yace tuni uwar jam'iyyar a jiha ta aike da bukatar kiran dukkan shugabannin ta a matakin kananan hukumomi da kuma mazabu domin tattara sunayen da tace kuma zata sake su ta hanyar wallafawa duk duniya ta gani.

Post a comment

0 Comments