Siyasar Kano: Salihu Sagir Takai ba zai fasa neman takarar Gwamna ba

Labarai daga 24blog
Kwankwaso ya dauko tsofaffin kwamishinonin sa Abba Kabir Yusuf da Ahmad Abdulsalam su fito takarar Gwamna da Mataimakin sa ne a Kano. Duk da haka Malam Salihu Takai ya nuna cewa ba zai fasa shiga zaben fitar da gwani da za ayi a PDP ba.
Kwamitin yakin neman zaben Takai ta tabbatar da cewa a shirye 'Dan takarar yake da ya goga da wanda Kwankwaso ya tsaida wajen neman tikitin Jam'iyyar PDP. A karshen makon nan ne aka tantance Takai a matsayin 'Dan takarar Gwamna a Kaduna.


Kwanaki ne dai Uwar Jam'iyya ta rushe Shugabancin PDP a Kano aka nada wani 'Dan Kwankwasiyya a matsayin Shugaban rikon kwarya. Wannan ya sa Shekarau ya koma APC amma irin su Takai su ka bi Kwankwaso su na sa ran samun tikiti.

Salihu Takai tsohon Kwamishi na a Gwamnatin Shekarau wanda ya dade yana neman Gwamna. Takai ya dade a PDP kafin Kwankwaso da jama’ar sa su bar Jam’iyyar APC kwanaki.