Online counter

Sauyin yanayi ke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa 'Kasashen Turai - Buhari

Sauyin yanayi ke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa 'Kasashen Turai - Buhari

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaba Buhari ya bayyana sauyin yanayi cikin jerin ababen da suke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa kasashen Turai. Sauran ababen kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana sun hadar da; rashin tsaro, ilimi da kuma nakasun kula da harkokin kiwon lafiya da sauransu.
Cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Mista Toni Iwobi, dan asalin kasar Najeriya dake rike da kujerar Sanata a majalisar dattawa ta kasar Italia.
Ganawar a ranar Alhamis din da ta gabata tsakanin shugaba Buhari ta Mista Iwobi ta gudana ne a wani bangare na daban da taron majalisar dinkin duniya karo na 73 dake ci gaba da gudana a birnin New York na kasar Amurka. 
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya gana tare da Mista Iwobi da kuma tawagar wakilan majalisar dattawan kasar ta Italiya, inda suka tattauna yadda sauyin yanayi ke haddasa barazanar ƙaura zuwa kasashen Turai a tsakankanin Matasan Najeriya.
Tawagar dattawan kasar Italiya ta kuma tattauna al'amurran da za su kawo karshen yadda ake ribatuwa da Tafkin Chadi wajen ƙaura da ba bisa ka'ida ba, inda kuma suka gabatarwa da shugaba Buhari shirye-shiryensu na ziyartar Najeriya na ba da jimawa ba.

Post a Comment

0 Comments