Online counter

Sai na cinye zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar PDP – Inji Makarfi

Sai na cinye zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar PDP – Inji Makarfi 

LABARAI DAGA 24BLOG
Labari ya zo mana daga Trust inda daya daga cikin masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi ya bayyana cewa shi zai yi nasara wajen samun tikitin Jam’iyyar PDP domin ya fi kowa cancanta.
Tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna yayi wannan jawabi ne a Jihar Kebbi lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman inda ya fadawa manyan PDP a Yankin cewa shi ne yake da abin da duk sauran ‘Yan takaran na PDP ba su da shi.
Sanata Ahmed Makarfi yace sauran ‘Yan takaran na PDP sun cancanta amma sai dai shi ne kurum ya iya rike Jam’iyyar adawar a lokacin da abubuwa su ka sukurkuce har ta kai PDP ta kawo inda ta ke a halin yanzu ake sha’awar ta.
Ahmed Makarfi ya bayyana cewa yayi aiki da jama’a da dama a PDP inda yace ya kawo ziyara Jihar Kebbi ne domin ya gana da jama’a ba wai don yayi kamfe ba. Makarfi ya kuma kara da cewa PDP za ta iya doke Buhari a 2019.

Post a comment

0 Comments