Online counter

PDP za tayi amfani da kai ne ta jefar - Tsohon gwamnan jam'iyyar

PDP za tayi amfani da kai ne ta jefar - Tsohon gwamnan jam'iyyar

-labarai daga 24blog
Tsohon gwamnan jihar Delta, Dr Emmanuel Uduaghan ya ce jam'iyyar PDP ba ta kulawa da 'ya'yan ta, da zarar ta gama cin moriyarsu sai ta yada su.
A hirar da akayi dashi a daren Juma'a a Channels tv, tsohon gwamnan ya dau alwashin fatattakar gwamna Ifeanyi Okowa da sauran masu rike da mukammai a jam'iyyar PDP a babban zaben 2019 mai zuwa.
A makon da ta gabata ne Uduaghan ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC inda ya ce mutane da yawa zasu biyo shi APC saboda a yanzu itace jam'iyyar da zata biya musu bukatunsu.
"Bari in fada maka wani abu. PDP ba ta taba kare 'ya'yanta ba. PDP za tayi amfani da kai ne amma duka abinda ya same ka babu wanda zai kula ka.
"Mutane za su fice daga PDP su shiga APC saboda a halin yanzu APC ne ka kawo kawo cigaba a yankin Niger-Delta. Saboda haka, zamu tattaro mutanen mu daga na yankin Kudu maso Kudu duk so shigo APC." Inji Uduaghan
Tsohon gwamnan kuma ya ce jam'iyyar APC ta yi yarjejeniya da jama'a Kudu maso Kudu kuma suna da mutane a cikin gwamnatin APC da zasu tabbatar cewa an cika ka'idojin yarjejeniyar wadda ake sa ran zata bawa yankin damar fitar da dan takarar shugaban kasa nan gaba.
Uduahgan ya yi na'am cewa jam'iyyar APC ba ta da karfi sosai a jihar a baya amma a yanzu shi da kansa zai yi jogoranci don ganin an wayar da kan jama'a kan alkhairan da ke tattare da mara wa APC baya kafin zaben 2019.
Ya musanta zargin da ake na cewa ya koma APC ne domin guje wa bincike EFCC. Ya ce bashi da abin boyewa saboda tun a baya hukumomin yaki da rashawa sun gudanar da bincike sosai a kansa kuma ba'a same shi da laifi ba.

Post a Comment

0 Comments