Online counter

PDP ta ga baiken sayawa fam din takara

PDP ta ga baiken sayawa fam din takara

-labarai daga 24blog 
Jam'iyyar adawa ta PDP tayi ikirarin cewa anyi amfani da wata kungiyar bogi ne domin siyawa shugaba Muhammadu Buhari fom din takarar zaben shugabancin kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan N45 miliyan.
Bayan siffanta wannan abin a matsayin 'yaudara da mutane sun gaji da ita', PDP ta ce lamarin na iya rage wa shugaba Muhammadu Buhari farin jini a wajen jama'a.
A sanarwa da ta fito daga Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce shugaba Buhari ba zai iya yaudarar mutane da sunan cewa yana tare da talakawa ba.
"Mutane sun farga sun gano cewa shugaban kasa da na kusa dashi suna rayuwa cikin daula, alhalin ya yi watsi da miliyoyin talakawa da suka amince dashi suka bashi amana a 2015.
Kazalika, PDP ta janyo hankalin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) cewa sayawa shugaba Muhammadu Buhari fam da kungiyar tayi ya ci karo da sashi na 91(9) na dokar zabe da ya ce "ba'a amince mutum ko kungiya ta bawa dan takara tallafin da ya haura N1 miliyan ba."
"Tunda shugaba Buhari bai fito fili ya nuna kin amincewarsa da sayan fam din da kungiyar tayi masa, ya kamata INEC ta gurfanar da shugaban kasa cikin sa'o'i 24 kamar yadda dokar zabe ya tanada," inji PDP

Post a comment

0 Comments