Online counter

PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark

PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark

LABARAI DAGA 24BLOG
Sanata David Mark ya kyautata zatonsa da cewa, jam'iyyar ta PDP ba za ta tarwatse ba koda kuwa bayan an kammala zabenta na fidda gwanin da zai rike mata tutar takarar kujerar shugaban kasa a 2019.
Yake cewa, akwai barazanar jin kunya da kuma shan takaici ga duk wanda ba su tashi sun farga ba kuma suke hasashen za a fuskanci mummunan rikici da rashin jituwa bayan an gudanar da zaben fidda gwanin takara na jam'iyyar.
Tsohon shugaban majalisar ya yi bugun kirji da cewa, sabanin rashin kyawun zato da hasashe da wasu mutane ke yi kan yadda jam'iyyar za ta kasance bayan zabenta na fidda gwani, jam'iyyar za ta kara karfafa ta fuskar hadin kai da mai karfin gaske.
Sanata David Mark ya na kuma da yakini da cewa, akwai goyon bayan mai tsananin amincin da jam'iyyar za ta bai wa duk wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin takarar kujerar shuagaban kasa kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.
tsohon shugaban majalisar ya yi wannan furuci yayin gabatar da jawabansa a babban ofishin jam'iyyar sa dake birnin Minna na jihar Neja, inda ya bayar da tabbacin sa kan cewa za a gudanar da tsaftataccen zabe da ya tsarkaka daga duk wani magudi ko rashin adalci yayin fidda gwani na jam'iyyar.

Post a comment

0 Comments