Online counter

Na zagaye da Buhari ne ke dagula masa lissafi - Inji wani jigo a APC

Na zagaye da Buhari ne ke dagula masa lissafi - Inji wani jigo a APC

- labarai daga 24blog
Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta dake ke kudu maso kudancin Najeriya Cif Ayiri Emami ya yi ikirarin cewa dayawa daga cikin wadanda ke zagaye da Shugaba Buhari sune ke dagula masa lissafi.
Cif Ayiri yace musamman ma ministocin gwamnatin Shugaba Buhari kwata-kwata basu don suka cigaban sa kuma a lokutta da dama sukan zamo tamkar 'yan hana ruwa gudu a sha'anin tafiyar da gwamnatin ta sa.
24blog ta samu cewa Cif Ayiri ya fadi hakan ne a lokacin dake zantawa da wakilin majiyar mu inda har ma ya bayar da misalin cikin ministocin Shugaba Buhari na wasanni da matasa watau Barista Solomon Dalung inda yace yana yakar gwamnatin ne ma a kai kai ce.
A wani labarin kuma, Labarin da ke iso mana yanzu na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode yanzu haka ya cikin wani gagarumin taron sirri da dukkan mukarraban sa a gidan gwamnatin jihar da ke a unguwar Ikeja.
Majiyar mu dai ta samu labarin cewa taron da ya kira yana da alaka ne da maganar fitar sa daga jam'iyyar APC mai mulki biyo bayan matakin da ta dauka na gudanar da zabukan fitar da gwani na kato-bayan-kato.

Post a Comment

0 Comments