Online counter

Musulmai na fuskantar tsangwama, kyama da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

Musulmai na fuskantar tsangwama, kyama da cin fuska a nahiyar turai – Bincike

LABARAI DAGA 24BLOG
A yayin taron an gabatar da wani rahoton wani bincike da aka gudanar a kasashen nahiyar turai guda takwas daga ciki harda kasar Faransa, Birtaniya da Jamus, inda rahoton ya nuna ana samun karuwar nuna tangwama ga Musulmai a turai.
“Wannan matsalar na gurbata zamantakewarmu a turai tare da sanya gaba a tsakaninmu” Inji wani dna majalisar dokokin nahiyar Turai dake wakiltar birnin Landan Jean Lambert, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Karin tsangwama ga musulmai ya danganta ne da maganganun da kafafen sadarwar ke yi dake rura matsalar tare da zantuttukan yan siyasa, dukkaninsu na kara ma turawa kwarin gwiwar kin jinin musulmai a yankunansu.” InJi rahoto.
wata masaniya mai suna Amina Easat-Daas dake aikin wayar da kan turawa game da illar nuna tsangwama da wariya ga Musulmai tana cewa “Bincikennan ya nuna yaduwar tsangwama ga Musulmai, tare da yadda ya shiga duka fannonin rayuwa da zamantakewa,
“Kokarinmu shine mu kawar da wannan matsalar ta hanyar wayar da kawunan mutanenmu tare da bayyana musu kyawawan halayen musulmai, zaman lafiyarsu tare da gagaruman gudumuwar da musulmai ke bayarwa a wajen inganta kasashenmu.” Inji ta.

Post a comment

0 Comments