Online counter

Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya

Manyan mutane 4 da suka sa labule da Buhari a taron majalisar dinkin duniya 

LABARAI DAGA 24BLOG
Buhari yayi wannan ganawarce da shuwagabannin bayan sun sanya labule inda suka goga gemu da gemi kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi bukatun junansu.
Daga cikin wadanda shugaba Buhari ya gana da su akwai shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo, wanda suka tattauna dashi game da barazanar da jama’an kasar Ghana ke yi ma yan kasuwan Najeriya mazauna Ghana.
A yayin ganawarsa da shugaban na Ghana, Buhari ya gayyaci ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama da mashawarcinsa akan al’amuran tsaro Babagana Monguno son su bada gudunmuwarsu a yayin tattaunawar.
Haka zalika Buhari ya goga gemu da gemu da shugaban kungiyar kasashen musulmai a duniya, OIC, Dakta Yousef Ahmed Al-Othaimeen, sai kuma shugaban majalisar dinkin duniyar kanta, Antonio Gutteres.
Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tattaunawar sirri da shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, shima anan sun tattauna batutuwan da suka shafi matsalar nuna wariya da jam’an kasar Afirka ta kudu ke nuna ma sauran yan Afirka da kuma hanyoyin hada kai game da matsalar tsaro.

Post a comment

0 Comments