Online counter

Maganin ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

Maganin ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar 'yan sanda ajihar Kwara ta samu nasarar cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a kwaryar garin Ilorin, makwanni biyu bayan kama aikin sabon kwamishinan 'yan sanda na jiahr, Mr. Bolaji Fafowora.
Da yake gabatar da 'yan fashin 19 da kuma 'yan shan jinin 11 a Ilorin, jiya Larana 26 ga watan Satumba, 2018, kwamishinan 'yan sandan ya ce wadanda ake zargin sun hada da wani mutumi mai shekaru 65 da ke gyara da kera bindugu, za a gurfanar da su a gaban kotu da zaran rundunar ta kammala bincike.
Fafowora wanda ya ce wasu daga cikin yankunan da 'yan fashin ke gudanar da aika aikarsu kafin rundunar ta samu nasrar cafke su sun hada da Ogele, layin Shao, Alapata, Kangu-Olunlade, Fate, Water View da kuma Sango.
Ya kara da cewa wasu daga cikin kayayyakin da rundunar ta kwato daga hannun 'yan fashi da kuma 'yan shan jinin sun hada da bindiga kirar Pistol da ake hadawa a Nigeria, bindigar harba ka labe, kananan gatari na fada, kayan tsubbace-tsubbace, tulin tabar wiwi, manyan wayoyin na'urar rarraba wutar lantarki da kuma mashina kirar Bajaj.
Haka zalike rundunar ta samu nasarar cafke wasu mutane biyar dake aiki a kungiyance, wadanda suka damfari mutane 6 kudi har N4m. Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun kware wajen damfarar jama'a ta hanyar basu kudaden kasashen waje na bogi, yayin da su kuma zasu karbi Naira a matsayin canji.

Post a Comment

0 Comments