Online counter

Labari da zafi zafi: Jam’iyyar APC ta haramtawa ministan Buhari takaran kujeran gwamna

Labari da zafi zafi: Jam’iyyar APC ta haramtawa ministan Buhari takaran kujeran gwamna


LABARAI DAGA 24BLOG
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta haramtawa ministan sadarwa, Barista Adebayo Shittu, takaran kujeran gwamnan jihar Oyo karkashin jam’iyyar bisa ga rashin yin bautar kasa.
Da farko, kwamitin tantance yan takaran jamiyyar APC ta tantance Shittu duk da cewan ta samu labarin cewa bai yi bautar kasa da yake wajibi ga dukkan dalibin Najeriya ba.
Amma daga baya, kwamitin gudanarwan jam’iyyar ta gana kan ayyukan kwamitin tantancewa kuma ta soke halaltawa Adebayo Shittu takara.
Irin wannan abu ne ya tilasta minister kudi Kemi Adeosun murabus daga kujeranta a makon da ya gabata

Post a comment

0 Comments