Online counter

Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

LABARAI DAGA TAKU HADIZA GABOM
A jiya, Juma'a ne tsohon gwamnan Kano, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya roki deliget din jihar Gombe suyi raba dai-dai tsakaninsa da Gwamna Dankwambo idan lokacin jefa kuri'a zaben fidda gwani na takarar PDP ya yi.
Kwankwaso ya yi wannna rokon ne a ranar Juma'a 28 ga watan Satumba a Gombe, yayin da ya ziyarci mataimakin gwamnan jihar, Mr Charles Iliya.
Ya shaida musu cewa ya ziyarci Gombe ne domin ya sanar da su niyyarsa na fitowa takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP gabanin gudanar da zaben fidda gwanin kana ya nemi goyon bayansu.
Kwankwaso ya ce yana da kwarewar gudanar da mulki saboda ya yi gwamna sau biyu kuma gashi ya yi Sanata hakan yasa ya ke ganin zai iya ceto Najeriya daga cikin mawuyacin halin da ta shiga.
"Na san kuna da dan takara a Gombe; amma za ku iya zabansa kuma nima ku zabe ni.
"Ba zan damu ba idan kun raba kuri'un ku gida biyu kun bani rabi, shi kuma dan takarar ku ku bashi rabin," rokon Kwankwaso ga deliget din Gombe.
A jawabinsa, mataimakin gwamnan Gombe, Iliyas ya tabbatar wa Kwankwaso cewar kuri'arsu ta PDP ne kuma ya yi masa fatan alheri da takararsa na shugabancin kasar.

Post a comment

0 Comments