Online counter

Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP

Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP


-labarai daga 24blog
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci sauran abokan takararsa a jam'iyyar adawa ta PDP suyi aiki tare da juna saboda kaucewa samun rashin jituwa tsakaninsu bayan babban taron jam'iyyar da za'a gudanar cikin watan Ocktoba.
Kwankwaso, ya yi bayar da wannan shawarar ne a taron da ya yi da 'yan jam'iyyar PDP a yau Laraba a Minna. Ya kuma ce dole dukkan 'yan takarar sun hada kai domin yiwa Najeriya hidima.
Ya kuma kallubalanci shugabanin jam'iyyar su yiwa dukkan 'yan takarar adalci wajen gudanar da zaben fitar da gwani domin yin adalci wajen zaben shine zai karfafa jam'iyyar har ta samu nasara a babban zaben da za'yi a watan Fabrairun 2019.
Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya cacaki gwamnatin APC inda ya ce bata tabbuka komai ba kuma har yanzu 'yan Najeriya ba su ga canjin da akayi musu alkawari ba tun a shekarar 2015.
"Canjin da aka kawo a Najeriya kawai shine yunwa, tashe-tashen hankula da rashin ayyukan yi," a cewar Kwankwaso.
Dan takarar kuma ya koka kan yadda titin Suleja zuwa Minna ta lalace duk da cewa titin yana daya daga cikin hanyoyin da jam'iyyar APC tayi alkawarin gyarawa a lokacin yakin neman zabe a 2014.
Ciyaman din PDP a jihar, Tanko Beji, ya tabbatarwa Kwankwaso cewa 'yan PDP reshen jihar Niger za su zabi dan takarar da zai inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Post a Comment

0 Comments