Online counter

kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

kwamitin tantance yan takara ta watsar da ministocin Buhari 2, 3 sun sha

LABARAI DAGA 24BLOG
Uwar jam’iyyar APC ce ta sanar da haka ta cikin wata sanarwa data fitar dake dauke da jerin sunayen yan takarkarunta da kwamitin tantance yan takara ta tabbatar dasu akan cewa sun cancanci tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
An bayyana sunayen ministocin da suka tsallake wannan mataki kamar haka; Usani Usani, ministan Nej Delta, Mansur Ali, ministan tsaro da kuma Mustapha Baba Shehuri karamin ministan ayyuka, lantarki da gidaje.
Ministan Neja Delta Usani na muradin zama gwamnan jahar Kros Ribas ne, yayin da Baba Shehuri ke muradin zama gwamnan jahar Borno, sai kuma shi Masur Dan Ali dake ganin ya dare mukamin gwamnan jahar Zamfara wanda hakan yasa a yanzu haka basa ga maciji da gwamnan jahar Abdul Aziz Yari.
Sai kuma ministocin da suka gagara tsallake wannan mataki da suka hada da ministan sadarwa Adebayo Shittu da yan takarar gwamna daya tilo daga jam’iyyar APC, Aisha Alhassan da aka fi sani da Maman Taraba, ministan al’amuran mata.
Mama Taraba na neman tsayawa takarar gwamnan jahar Taraba ne, yayin da Adebayo Shittu ke son tsayawa takarar gwamnan jahar Oyo, sai da kwamitin ta bayyana dalilin rashin amincewa da Shittu shine saboda bai yi bautar kasa ba bayan ya kammala digirinsa na farko, amma basu bayyana dalilin yin watsi da Aisha Jummai ba.

Post a comment

0 Comments