Online counter

kungiyar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a

kungiyar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a

LABARAI DAGA 24BLOG
rundunar yansandan dake yak yan fashi, F-SARS ne ta samu nasarar kama yan fashin a lokacin da ta tare wata mota kirar Mercedes Benz ML350 akan titin Hadeja, ashe motar kanta satota aka yi daga garin Maska na jahar Nassarawa.
Daga cikin wadanda ke cikin motar akwai Kenneth Adam, Ali Jafaru, Abdulkadir Shaka da Aliyu Audu, mazauna garin Masaka na jahar Nasarawa da rukunin Gunduwawa na jahar Kano, kamar yadda kaakain Yansanda SP Magaji Majia ya tabbatar.
Majiya yace yan fashin sun kai farmaki ne a garin Maska a ranar 22 ga watan Satumba, inda suka kwace ma wani mutumi motar Mercedes Benz ML350 da wasu kayayyaki.
Hakazalika Majia yace sun samu nasarar kama wasu tarin ganyen wiwi a unguwar Tudun Wazirchi da unguwar Badawa na jahar Kano, wanda acewarsa darajar wiwin ta kai naira miliyan 6.6.
A wani labarin kuma, DSP Majia ya bayyana cewa a ranar 19 ga watan Satumba da misalin karfe 3 na rana sun kama wasu matasa guda biyu Dangaja da Lado a yayin da suka tare wani mutumi akan titin Audu Bako inda suka kwace masa kudi naira dubu dari biyar, sa’annan suka raunatashi.

Post a comment

0 Comments