Online counter

Kungiyar kasashen Turai zata saka ido a kan zaben fitar da dan takarar PDP

Kungiyar kasashen Turai zata saka ido a kan zaben fitar da dan takarar PDP

LABARAI DAGA 24BLOG 
PDP zata gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasa a garin Fatakwal, jihar Ribas, ranar 6 da 7 ga watan Oktoba.
Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya shaidawa manema labarai a jiya, Asabar, cewar jam'iyyar na iya bakin kokarinta domin ganin ta gudanar da zaben fitar da dan takarar cikin nasar
Ologbondiyan ya yi zargin cewar jam'iyyar APC mai mulki na kokarin haddasa rikici a cikin jam'iyyar. Amma ya ce PDP ba zata bari wani abu ya hana ta yin nasara ba.
"Zamu gudanar da taron gangami cikin nasara kuma ba tare da rabuwar kai ba kuma zamu fitar da dan takarar da duk 'yan Najeriya zasu karbe shi hannu biyu.
"Kungiyar kasashen Turai (EU) ta nuna sha'awar saka ido a zaben mu na cikin gida. Muna iya bakin kokarinmu don gudanar da sahihin zabe na adalci.
"Za a nuna taron kai tsaye a gidajen talabijin," a cewar Ologbondiyan.
Ya kara da cewar PDP ba zata bari wani mutum ya yi kokarin juya akalar taron domin bawa wani dan takara fifiko ba.
Za a gudanar da zaben fitar da dan takarar ne tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata David Mark, tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang da tsohon minista a gwamnatin Jonathan, Tanimu Turaki.

Post a comment

0 Comments