Kenya: Ana zargin gwamna da kashe budurwarsa mai ciki

Ana tuhumar gwamnan wani yanki a Kenya Okoth Obado, da taimakawa da kuma sa hannu wajen kisan gillar da aka yi wa wata tsohuwar budurwarsa daliba mai ciki.
Gwamnan, wanda ke da iyali ya ki amincewa da tuhumar da ake masa.
An kama Mista Obado bayan shafe kwanaki da jama'ar yankin suka yi suna nuna fushinsu bayan da aka gano gaawar Sharon Otieno, mai shekara 26 a daji.
Wani bincike da aka yi a gawarta ya nuna cewa an yi mata fyade ne sannan aka caka mata wuka a wuya da ciki da kuma sau takwas. Ta rasa dan da ke cikinta duk a wannan hari.
A yanzu ana tsare Mista Obado gwamnan yankin Migori, har sai an samu sakamakon bukatar bayar da belinsa da aka shigar a ranar Talata.
Mahaifiyar Otieno Melida Auma ta yi ta kuka a kotu, tana kokarin kar damuwarta ta sanya ta a wani hali, a cewar Jaridar Kenya Standard.
A wata sanarwa da babban mai shigar da kara na Kenya ya fitar tun da farko, Noodin Haji ya ce ya kuma bayar da umarnin a gurfanar da wasu mataimakan gwamnan na musamman biyu - daya kan ksan gilla daya kuma kan taimakawa a yi kisan.
"Sharon da dan tayinta sun rasa rayukansu a wannan kisan gillar da aka yi musu. A don haka ofishina ya sha alwashin tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi da aikata wannan abu, a kuma hukunta su, in ji," Mr Haji.
Yaya binciken ya kasance?
Kisan gillar da aka yi wa Otieno ya bata ran al'ummar Kenya musamman tun bayan da wani dan jarida ya yi zargin cewa Ms Otieno ta tuntube shi kan batun cewa wani yana nemanta.
Mista Odour ya ce sun hadu kuma an sace su a ranar 3 ga watan Satumba.
Ya kara da cewa ya samu ya fado daga cikin motar da ke tsananin gudu, inda ya bar Ms Otieno tare da wadanda suka sace su din.
Kwana biyu bayan nan ne 'yan sanda suka samu gawarta a wata duhuwa kusa da wani karamin gari Oyugis a yammacin Kenya.
Daga baya 'yan sanda sun motar da ake zargin maharan sun yi amfani da ita.
Bincike ya kuma gano cewa akwai alaka mai karfi tsakanin Mista Obado da Ms Otieno, wanda har aka samu ciki a dalilin hakan,al'amarin da bai yi wa gwamnan dadi ba.

Me gwamnan ya ce?
A yayin da Mr Obado ya zamo shi ne wanda bincike ya fi mayar da hankali a kansa, sai ya yi watsi da zargin hannu a kisan Otieno.
An ruwaito shi yana cewa: "A matsayina na dan kasa mai bin doka, ina so na yi bayani cewa ba ni da hannu ko kadan a kisan Sharon."
A makon da ya gabata ne lauyansa cewa gwamnan ya yi mu'amala da Ms Otieno a baya, amma bai tabbatar ba ko tana da cikinsa ko a'a.