Online counter

Kayar da Buhari ba shine zai magance matsalar Najeriya ba - Fani Kayode

Kayar da Buhari ba shine zai magance matsalar Najeriya ba - Fani Kayode

- Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Cif Fani-Kayode ya ce kayar da Buhari ba zai magance matsalolin Najeriya ba
- Jigon na jam'iyyar PDP ya ce yiwa tsarin rabon arzikin kasa garambawul shine kadai mafita
- Ya jadada cewa dukkan wanda aka zabe muddin bai yi garambawul din ba zai cigaba da fuskantar matsaloli
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Femi Fani-Kayode ya ce kawar da shugaba Muhammadu Buhari daga karagar mulki ba shine abinda zai warware matsalolin Najeriya ba.
A cewarsa, hanyar da za'a bi domin warware matsalolin kasar shine idan an amince da a zaune waje daya ayi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawal ta yadda za'a rika raba dai-dai na arzikin da kasar ke samu.
Fani-Kayode ya fadi wannan sakon ne a shafinsa na sada zumunta a Facebook yayin da yake aike wa masu bibiyar shafinsa barka da sabuwar wata.
Ya ce, "Zabe na karatowa kuma mutane da dama suna son dare wa kujerar shugaban kasa. Wasu son na da nagarta wasu kuma basu dashi. Sai dai gaskiyar lamarin shine ba za'a iya magance matsalar Najeriya kawai don ayi zaben shugaban kasa ba.
"Duk wanda ke tunanin kawar da Buhari kadai ce zata magance matsalolin kasarmu tabbas bai fahimci matsalolin kasar ba, sai mun kara aikata wani abun.
"Maganar gaskiya shine za'a magance matsalolin Najeriya ne kawai idan an yiwa tsarin rabon albarkatun kasa garambawul. Duk wani abu da za'ayi wanda ba hakan ba kawai bata lokaci ne.
"Idan ba haka aka aikata ba, duk ma wanda ya karbi mulkin ko ba Buhari bane zai cigabda da fuskantar dukkan matsalolin da muke fuskanta a yanzu. Ubangiji ya bamu basira da fahimta da hangen nesa.

Post a comment

0 Comments