KAYANA HADI

  • Wake
  • bushasshen rogo
  • Dawa
  • Kuka
  • Kanwa

Yadda ake sarrafawa
1. Da farko za a hada wake da rogo da dawa a niko, amma rogon ya fi su yawa
2. A jika kanwa a cikin ruwan da za a yi kwabin da shi
3. Idan aka niko sai a tankade a zuba kuka a ciki a kwaba da ruwan kanwar
4. A dora tukunyar ruwan zafi a wuta, idan ya tafasa, sai ana saka kullin dan waken kanana kanana
5. Ana ci da yaji da mai da kwai da tumatir da albasa