Online counter

Karshen su yazo: 'Yan Boko Haram sun fara kashe kan su da kan su

Karshen su yazo: 'Yan Boko Haram sun fara kashe kan su da kan su

LABARAI DAGA 24BLOG
A yayin da jami'an tsaron Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ke cigaba da fatattakar 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram musamman ma a dazukan da suke neman mafaka, kawunan 'yan ta'addan na cigaba da rabuwa a tsakankanin su.
Labarin da muka samu da dumin sa yanzu dai shine wasu daga cikin 'yan ta'addan dake a bangaren da sukayi mubayi'a ga Mamman Nur sun kashe daya daga cikin manyan kwamandojin su mai suna Ali Garga bisa zargin sa da sukayi da cin amana.
Ali Garga ya shirya tsaf ne domin kubutar da wasu daga cikin wadanda 'yan Boko Haram din suka kama ne har su 300 sannan kuma ya mika wuya don karin kan sa ga jami'an sojoji kafin asirin sa ya tonu a wurin 'yan uwan sa.
Mun samu dai cewa biyo bayan tonuwar asirin nasa ne dai sai 'yan uwan nasa suka kashe shi don tsabar rashin tausayi da imani a ranar Alhamis din da ta gabata a can maboyar ta sa kamar dai yadda majiyar mu ta shaida mana.
Shi dai Ali Garga bafullatani ne daga jihar Taraba da aka tilastawa shiga kungiyar ta'addancin ta Boko Haram a shekarun baya biyo bayan sace masa garken shanu da akayi.

Post a Comment

0 Comments