Online counter

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Osun, Folasade Odoro, ta bayyana hakan a wani jawabi da ta fitar ga manema labarai a yau, Alhamis.

LABARAI DAGA 24BLOG
Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Osun, Folasade Odoro, ta bayyana hakan a wani jawabi da ta fitar ga manema labarai a yau, Alhamis.
Ta bayyana cewar an kama mutanen ne a karamar hukumar Orolu, daya daga cikin kananan hukumomin da ake maimaita zaben gwamnan jihar.
Kazalika ta bayyana cewar an samu wadanda kama din da katin shiadar zama mambobin jam’iyyar PDP amma kuma suna sanye da alamar dake nuna cewar su ma’aikatan INEC. Sannan ta kara da cewar suna amfani da kayan jami’an hukumar INEC domin shiga wuraren da bai kamata bad a kuma samun dammar taba kayan aikin zabe
Bayan kayan hukumar INEC, an same su da Karin wasu kayan irin na masu saka ido lokacin gudanar da zabe.
Odoro ta kara da cewar babu gaskiya a cikin rahoton da ake yadawa cewar sun kama wasu masu aikin saka ido a zaben raba gardama na Osun tare da bawa mutanen jihar da masu ruwa da tsaki tabbacin cewar hukumar ‘yan sanda zata samar da isashshen tsaro domin ganin an kamala zaben lami lafiya.
Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

Zaben Osun: ‘Yan sanda sun kama ‘yan PDP dake sojan gona a matsayin jami’an INEC, hoto

Post a comment

0 Comments