Online counter

Ka da mu bari siyasa ta raba kan mu inji Sanata Dino Melaye

Ka da mu bari siyasa ta raba kan mu inji Sanata Dino Melaye

LABARAI DAGA 24BLOG
Sanata Dino Melaye wanda yake wakiltar Jihar Ko a Majalisar Dattawa ya nemi jama’a su ajiye banbancin da su ke da shi a gefe guda domin ganin Najeriya ta cigaba. Melaye yayi wannan jawabi ne a wajen wani taro a makon jiya.
Kungiyar Okun Development Initiatives watau ODI ne ta shirya wani taro domin karrama Sakataren yada labaran Jam’iyyar PDP da kuma Kwamishinan karbar korafin jama’a na Jihar Kogi Olusuyi Otitoju a Garin Abuja.
A wajen taron Dino Melaye ya nemi mutanen Okun da su guji yin abin da zai raba kan su saboda wani ‘dan kankanin abu da za a ba su na Duniya. Fitaccen ‘Dan Majalisar ya nemi jama’a su yi hattara ka da siyasa ya raba su.
A wajen taron da aka yi a babban Birnin Tarayya Abuja, Sanata Melaye ya yabawa Sakataren yada labaran Jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan wanda yana cikin wadanda aka karrama. Melaye yace Kola Ologbondiyan ya gyara PDP.
‘Dan Majalisar da ya sauya sheka daga APC zuwa PDP kwanaki ya jinjinawa Kola Ologbondiyan wanda yace ya sauyawa PDP fuska tun da ya zama Kakakin ta. A cewar ‘Dan Majalisar, Ologbondiyan mutum guda ne tamkar dubu.
Cif Victoria Awomolo yayi kira Gwamnati ta kafa Kotu na musamman wajen maganin miyagu a wajen taron. Victoria ne Shugaban wadanda su kayi magana wajen wannan taro da aka yi a Ranar Juma’a.

Post a Comment

0 Comments